IQNA

An Daikile Wani Shirin Kai Harin Ta’addanci A Tunisia

23:37 - April 02, 2020
Lambar Labari: 3484676
Tehran (IQNA) Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya a kasar Tunisia sun bankado wani shirin kungiyar Daesh na kai wasu munanan hare-hare a kasar.

Ma’akatar harkokin cikin gidan kasar Tunisia ta sanar a jiya cewa, jami’an hukumar tsaro ta farin kaya a kasar, sun samu nasarar bankado wani shirin kai harin ta’addanci da kungiyar ‘yan ta’addan daesh ta shirya a cikin kasar.

Bayanin ya ce an samu nasarar cafke mutumin da shi ne zai aiwatar da harin, inda a halin yanzu yake harhada kayayyaki da kuma sanadaran za a yi amfani da su wajen kaddamar da harin.

Bisa ga bayanin da hukumar ta samu daga mutumin da aka kame, wanda mamba ne na kungiyar daesh, ya tabbatar da cewa suna da shirin kai harin ne a cikin watan Ramadan, kuma sun yi amfani da wannan damar ne a halin yanzu, lokacin da gwamnati da jami’an tsaro suka shagaltu da batun corona, domin yin cikakken na kaddamar hari mafi muni.

Jami’an tsaron dai su ne suna ci gaba da bin kadun lamarin, domin tabbatar da cewa an samu nasarar damke dukkanin wadanda suke da hannu a cikin shirin.

 

3888504

 

Abubuwan Da Ya Shafa: saudiyya ، tabbatar da ، cewa ، damke ، daesh ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha