IQNA

Amnesty Int. Ta Bukaci A Yi Bincike Kan Mutuwar Mutane A Yamutsin Da Aka Yi

23:58 - April 05, 2020
Lambar Labari: 3484682
Tehran (IQNA) Kungiyar Amnesty Int, ta bukaci a yi bincike bayan jami’an gidan yari a Kaduna suka sanar da cewa fursinoni hudu ne suka mutu a boren da suka yi a ranar Talatar da ta gabata.

Rahotanni sun ce hukumomin gidajen yarin sun fidda wannan bayanin ne bayan da kafafen yada labarai da wasu kungiyoyin kare hakkin bil’adama suka tashi tsaye don gano gaskiyar abinda ya faru a babban gidan yari na Kaduna a ranar Talatar da ta gabata.

Kafin haka dai hukumomin sun musanta cewa akwai wanda ya mutu a boren na ranar Talata. Sai dai a ranar juma’ar da ta gabata ce kakakin hukumar Austin Njoku ya tabbatar wa ‘yan jarida cewa fursinoni hudu sun mutu a boren.

Amma dukkansu wadanda aka yankewa hukuncin kisa ne. Sannan ya kara da cewa wasu daga cikin jami’an tsaron gidan yarin sun ji raunuka, ai dai wasu bayanai da ba na hukumomi na cewa mutane 8 suka mutu. 

Kungiyar kare hakkokin muuslmi da ke da mazauni a birnin London ita ma ta yi kira da da a gudanar da bincike kan lamarin.

Gidan kason Kaduna dai a nan ne ake tsare da Sheikh Ibrahim Zakzaky da mai dakin malama Zinat, inda magoya bayan harkar musulunci ke nuna damuwa kan halin da suke ciki.

3889207

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Kaduna ، gidan kaso ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha