IQNA

Amurkawa Sun Girmama Wani Likita Musulmi Wanda Ya Samar da Na’urar Taimaka Ma Lumfashi

23:57 - April 13, 2020
Lambar Labari: 3484709
Tehran (IQNA) Mutanen Amurka sun girmama wani likita musulmi wanda ya samar da wata na’ura wadda take taimaka ma masu fama da corona wajen lumfashi.

Shafin yada labarai na arabicpost ya bayar da rahoton cewa, mutanen Amurka sun girmama likita Saud Anwar, wanda ya samar da na’ura mai taimakawa wajen lumfashi, domin amfanin masu fama da matsalar corona.

Bayanin ya kara da cewa, Dr. Saud Anwar wanda ya yi karatu a jami’ar Karachi da ke kasar Pakistan, ya karanci likitanci kuma ya kware a bangaren cututtukan kwada, daga bisani ya koma Amurka da zama baki daya, inda yake gudanar da aikinsa.

Bayan gargadin da gwamnan New York ya yi a kwanakin baya kan karancin na’urorin da suke taimakawa wajen lumfashi a asibitocin da ake kwanatar da masu fama da matsalar corona, Dr. Saud Anwar ya shiga gudanar da aikin samar da wata na’ura wadda za ta taimaka  a wannan bangaren.

A halin yanzu na’urar da ya samar an fara aiki da ita wajen taimaka ma masu matsalar corona a kasar Amurka.

3891329

 

 

captcha