IQNA

Kiristoci Da Musulmin Saliyo Sun Fitar Da Littafi Na Hadin Gwiwa Kan Yaki Da Corona

23:46 - April 16, 2020
Lambar Labari: 3484717
Tehran (IQNA) a kasar Saliyo mabiya addinan musulunci da kiristanci sun fitar da littafi na hadin gwiwa kan yaki da cutar corona.

Shafin yada labarai na politico SL ya bayar da rahoton cewa, jagororin mabiya addinan musulunci da kiristanci a kasar Saliyo, sun fitar da wani littafi na hadin gwiwa a tsakaninsu kan yaki da cutar corona a fadin kasar.

A cikin wannan karamin littafi an yi ishara da bayanai na dukkanin addinan biyu kan hanyoyion da za a bi wajen yaki da cutar corona.

Ramadan Jello daya daga cikin jagororin mabiya addinin musulunci a kasar Saliyo ya bayyana cewa, a addinin muslunci ayoyin kur’ani mai tsarki sun yi ishara da bin shawarwarin masana kan kowane irin lamari, da kuma tambayrsu abin yi.

Ya ce saboda hakan batun corona hanyar kiyaye kamuwa da ita ce bin kai’idoji na masana kiwon lafiya.

Shi ma a nasa bangaren Soton Koruma daya daga cikin jagororion mabiya addinin kirista ya yi ishara da cewa,a  cikin littafin Linjila an umarci mutane da su bi umarnin masana kan dukkanin lamurra, wanda kuma kiyaye umarnin likitoci kan batun corona shi ne mafita.

3891985

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: cutar corona ، Saliyo ، jagororin ، musulmi ، kirista ، hanyoyin
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha