IQNA

Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Yi Kira Ga Isra’ila Da Saki Fursunonin Falastinawa

23:57 - April 17, 2020
Lambar Labari: 3484720
Tehran (IQNA) kungiyar kasashen larabawa ta yi kira ga Isra’ila da ta saki fursunonin Falastinawan da take tsare da su a cikin wannan yanayi na corona.

Kamfanin dillancin labaran Palestine ya bayar da rahoton cewa,a  cikin bayanin da kungiyar kasashen larabawa ta fitar, ta bayyana cewa dole ne Isra’ila ta dauki matakai na sain falstinawan da take tsare da su, saboda halin da ake ciki na rashin tabbas dangane da corona.

Bayanin ya ce babu wani dalili da zai sanya Isra’ila ta ci gaba da tsare dubban Falstinawa  a cikin gidajen kaso, alhali babu wani tabbaci kan ba su kariya daga kamuwa da cutar corona, wadda za ta iya yin jalin da dama daga cikinsu.

Kungiyar kasashen larabawa ta ce tana kiran kungiyoyi na kasa da kasa da majalisar dinkun duniya da sauran gwamnatocin kasashen duniya, da su matsa lamba kan Isra’ila a kan wannan batu.

Yanzu haka dai akwai Falastinawa fiye da dubu biyar da Isra’ila ta garkame a gidajen kurkuku, akasarinsu kuma bisa tuhumomi ne na nuna adawa ga Isra’Ia, yayin da kuma wasu babu wata tuhuma a kansu.

 

 

 

3892162

 

 

captcha