IQNA

Dakarun Iraki Suna Ci Gaba Da Fatattakar Sauran ‘Yan ta’adda A Kasar

23:59 - April 17, 2020
Lambar Labari: 3484721
Tehran (IQNA) dakarun kasar Iraki suna ci gaba da bi sawun ‘yan ta’addan Daesh a sassa daban-daban na kasar domin karasa su.

Kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, dakarun hadin gwiwa na yaki da ta’addanci a kasar Iraki suna ci gaba da fattatakar ‘yan ta’addan da suka yi saura a wasu na kasar.

Rahoton ya ce dakarun Iraki sun hakala wani jigo na kungiyar Daesh a garin Baakuba da ke cikin lardin Dayali da ke yammacin kasar, tare da jikkata wasu.

Wannan ya zo bayan farmakin da dakarun suka kai ne a wani wuri da ‘yan ta’addan suka buya, bayan samun bayanan sirri kan maboyar tasu, inda da farko aka musayar wuta da su, daga bisani kuma suka mika kai.

Dakarun hadin gwiwa na kasar Iraki da suka hada da sojojin gwamnati da kuma dakarun sa-kai na al’ummar Iraki na Hashd Shaabi, sun fara kaddamar da hare-hare a baya-bayan nan ne, sakamakon yadda kungiyoyin ‘yan ta’adda suke neman sake farfadowa a kasar, tun bayan da al’ummar kasar suka nemi Amurka da fice daga kasar tasu.

 

3892165

 

captcha