IQNA

Sallar Tarawihi A Msallacin Manzo Ba Tare Da Mahalrta Ba

23:06 - April 18, 2020
Lambar Labari: 3484723
Tehran (IQNA) za  agudanar da sallar tarawihia  bana a masallacin manzon Allah (SAW) ba tare da mahalarta ba.

Jaridar Albayan ta UAE ta bayar da rahoton cewa, Jam’an Asiri shugaban cibiyar kula da haramin makka da na Madina ya bayyana cewa, har yanzu ana ci gaba da hana mutane shiga masallatan biyu masu alfarma.

Ya ce suna ci gaba da gudanar da yin feshi na maganin da ke kashe cututtuka a masallatan biyu na  Makka da Madina, idan hali ya bayar za a yi bar mutane su ci gaba da zuwa, idan kuma bah aka za a ci gaba da killace masallatan.

Shi ma a nasa bangaren babban mai bayar da fatawa na masarautar saudiyya Abdulaziz Al Sheikh ya bayyana cewa, bisa la’akari da yanayin da ake ciki na cutar corona, mutane su yi sallar tarawihia  cikin gidajensu.

Dangane da salar idi kuma ya bayyana cewa, idan wannan yanayi na corona ya ci gaba har zuwa salla idin fitir, ba za a gudanar da sallar idi a masallatan kasar ta Saudiyya ba.

 

 

 

3892392

 

 

captcha