IQNA

Za A Fara Wani Shiri Na Yada Karatun Kur’ani Tare Da Tarjama A Lokaci Guda A Saudiyya

23:54 - April 22, 2020
Lambar Labari: 3484734
Tehran (IQNA) ana shirin fara aiwatar da wani tsari na watsa karatun kur’ani tare da tarjamarsa a lokaci guda a cikin watan Ramadan a kasar saudiyya.

Jaridar Ukaz ta Saudiyya ta bayar da rahoton cewa, yanzu haka ana shirin fara aiwatar da wani tsari na watsa karatun kur’ani tare da tarjamarsa a cikin harsunan Ingilishi da Faransanci a lokaci guda a cikin watan Ramadan.

Bayanin y ace karatun zaa gudanar da shi kamar yadda aka saba, inda za arika saka shi a kafofin sadrawa tare da sautuka na makaranta daban-daban daga cibiyoyin kur’ni na haramin Makka dakuma masallacin manzo da ke Madina.

Wannan shiri dai an saba gudanar da shia  kowace shekara, amma ana saka karatun kur’ani kawai ba tare da tarjama ba, amma a wannan karon shirin zai dauki wani salo domin amfanin masu fahimtar wadannan harsuna biyu.

Bayanin ya ce akwai 'yan kasashen Afrika da 'yan kasashen Asia da suke zaunea  kasar wadanda basa fahimtar larabaci, wanda tarjamar kur'ani zai yi musu amfani matuka.

 

3893310

 

captcha