IQNA

23:56 - April 24, 2020
Lambar Labari: 3484740
Tehran (IQNA) shugaba Rauhani na Iran ya aike da sakon taya murnar shiga watan Ramadan mai alfarma zuwa takwarorinsa na kasashen musulmi.

A cikin bayanin da ofishin shugaba Rauhani ya fitar a yau Juma’a, an bayyana cewa shugaban kasar ta Iran ya aike da skon taya murnar shiga watan Ramadan mai alfarma mai alfarma, zuwa ga dukkanin shugabanni na kasashen musulmi.

Shugaba Rauhani a cikin sakon nasa ya yi fatan alhairi ga dukkanin shugabannin kasashen musulmi da kuma al’ummomin kasashensu, tare da bayyana wannan lokaci na ibadar azumi da cewa lokaci ne mai matukar muhimmanci ga dukkanin musulmi, tare da bayyana shi a matsayin wata babbar dama ta yin addu’a da rokon Allah ya kawo karshen annobar corona a dukkanin kasashen musulmi da ma sauran kasashen duniya baki daya.

 

 

 

 

3893811

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: shugaba rauhani ، na kasar Iran ، aike ، sakon ، taya murna ، watan ramadan ، azumi ، cutar corona
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: