IQNA

Magatakardan MDD Ya Isar Da Sakon Murnar Shiga Ramadan Da Ayar Kur’ani

23:57 - April 24, 2020
Lambar Labari: 3484741
Tehran (IQNA) babban sakataren majalisar dinkin duniya ya isar da sakon taya murnar shiga watan Ramadan mai alfarma ga al’ummomin muuslmi na duniya.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a cikin sakon nasa, Antonio Guterres babban sakataren majalisar dinkin duniya, ya bayyana azumin wannan shekara da cewa ya samu muuslmin duniya a cikin wani mawuacin hali na bullar cutar corona.

Ya ce zai amfani da wannan damar domin yin kira zuwa ga zaman lafiya da sulhu kamar yadda addinin musulunci ya koyar, inda ya yi ishara da ayar kur’ani mai tsarki da ke magana kan sulhu, inda ayar ke cewa da manzo idan makiya sun karkata zuwa ga sulhu, kai ma ka karta zuwa ga yin sulhu da su, (surat Anfal aya 61).

Guterres ya ce bisa koyarwa ta addinin muslunci, an karfafa karamci da ‘yan adamtaka da kuma tausayi, wadanda su ne tushen zaman lafiya a tsakanin ‘yan adam baki daya. A kan haka ya ce yana kira da a yi amfani da wannan koyarwa musammana  cikin wannan wata, domin dakatar da duk wasu tashe-tashen hankula.

Haka nan kuma ya jaddada wajabcin hada karfi da karfe a tsakanin dukkanin al’ummomin duniya domin yaki da cutar corona wadda ta addabi duniya baki daya.

 

3893609

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha