IQNA

23:54 - April 26, 2020
Lambar Labari: 3484747
Tehran (IQNA) Sayyid Abbas Musawi kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya mayar da martani kan shirin Isra’ila na mamaye wasu yankunan Falastinawa.

Shafin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayar da bayanin cewa, Sayyid Abbas Musawi kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya bayyana sabon shirin Isra’ila na mamaye wasu karin yankunan Falastinu na shekarar 1948 da ke gabar yamma da kogin Jordan da cewa, wannan yana daga cikin shirin Trump da ake kira da mu’amalar karni.

Ya ce lokaci ne da bangarori na kasa da kasa da suka hada da majalisar dinkin duniya da sauran kasashe su sauke nauyin da ya rataya a kansu na kare hakkokin al’ummar Falastinu.

Musawi ya ce Isra’ila tana son ta yi amfani da damar da ta samu a lokacin da duniya ta shagaltu da batun yaki da annobar corona, ita kuma ta mamaye wasu Karin yankunan Falastinawa.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya ce, al’ummar Falastinu suna da bukatuwa zuwa ga taimakon al’ummomin duniya a dukkanin bangarori, da hakan ya hada da dakatar da mamaye musu yankuna da Isra’ila ke yi, da kuma yaki da cutar corona.

 

3894388

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Iran ، martani ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: