IQNA

Gasar Kur’ani Ta Daliban Jami’a A Masar

19:11 - May 01, 2020
Lambar Labari: 3484757
Tehran (IQNA) za a gudanar da gasar kur’ani ta daliban jami’a ta kasar Masar.

Shafin yada labarai na almalnews.com ya bayar da rahoton cewa, Muhammad Usman Alkhashab shugaban jami’ar birnin Alkahira ya sanar da cewa, dalibai suna damar aikewa da sakonninsu na karatun kur’ani da aka dauki sautinsa tsawon mintuna uku a adireshin youth. cu. edu.Eg2020@gmail.com daga nan zuwa ranar 20 ga watan Ramadan da muke ciki.

Ya ce daliban za su iya daukar kowace kira’a suke bukata daga cikin kira’oi 7 da ake da su.

Haka nan kuma shugaban jami’ar Kahira ya ce za a bayar da kyatuka ga wadanda suka zo na daya da na biyu da na uku, inda za su samu kyautar fan dubu 10, da dubu 5, da kuma dubu 3.

Kuma za su iya kwaikwayon fitattun makaranta kamar su sheikh Muhammad Refat, sheikh Alhusri, Sheikh Alminshawi, sheikh Abdulbasit, sheikh Mustafa Isma’il, da sheikh Mahmud Alkhashab.

 

 

 

3895630

 

 

 

 

captcha