IQNA

Nu’aina: Muna Shirin Kafa Wata Babbar Jami’ar Kur’ani Ta Duniya

16:18 - May 05, 2020
Lambar Labari: 3484766
Tehran (IQNA) babban makarancin kur’ani na kasar Masar Ahmad Nu’aina ya bayyana cewa suna shirin kafa wata bababr jami’ar kur’ani ta duniya.

Shafin yada labarai na Yaum Sabi ya bayar da rahoton cewa, Masar Ahmad Nu’aina ya bayyana cewa, bisa la’akari da yawan mutanen da suke da shirin zama masana a bangaren kur’ani dole nea  dauki mataki na taimaka msuu.

Ya cea  halin yanzu akwai na kafa wata bababr jami’a ta kur’ani da dukkanin ilmominsa, wadda za ta kasance ta duniya ce baki daya.

Wanann jami’a za ta kasance ta mayar da hankali ne ga ilmomin kur’ani mai tsarkia  dukkanin bangarori, kama daga sanin ilimin kira’a, da bangarorinta da kuma ilimin hukuncin karatun da sauransu.

Haka nan kuma za a dauki dalibai daga bangarori na duniya da suke da shawa a wannan fage, inda za a sanar da dukkanin tsare-tsaren wanann jami’a da zaran an kammala shirin farko.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3896366

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: bangarori
captcha