IQNA

Shaukin Mutanen Mauritania Na Zuwa Masallaci

14:55 - May 10, 2020
Lambar Labari: 3484784
Tehran (IQNA) bayan da mahukuntan kasar Mauritania suka sanar da sassauta dokar hana taruka daruruwan mutane sun nufi masallaci domin salla.

Tashar Euro News ta bayar da rahoton cewa, sakamakon saarwar da aka bayar na bude masallatai a birnin Nuwakshot na Mauritania, jama’a da dama sun nufi masallatai domin sallar Juma’a.

A ranar Laraba da ta gabata ce gwamnatin kasar Mauritania ta sanar da cewa ta sassauta dokar takaita zirga-zirgar jama’a, domin bayar da dama ga mutane su gudanar da harkokinsua  cikin wannan wata.

Sai dai bayan bayar da wannan sanarwa an bayyana cewa dole ne mutane su kiyaye kaidoji na kiwon lafiya, da hakan ya hada das aka takunumin fuska da wanke hannuwa.

Jama’a da dama a kasar ta Mauritaniya dai sun yi murna da wannan mataki da mahukuntan kasar ta Mauritania suka dauka.

https://iqna.ir/fa/news/3897736

 

 

 

captcha