Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar rahoto daga kasar Afrika ta kudu cewa, za a gabatar da jawabai na ranar, amma ta hanyar hotunan bidiyo kai tsaye, inda Zahra Khomenei diyar marigayi Imam Khomeni za ta kasance cikin masu gabatar da jawabi, da kuma Amir Abdullahian mataimakin shugaban majalisar dokokin Iran.
Baya ga haka kuma Mandela Mandela jikan tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu Nelson Mandela na daga cikin masu jawabi a ranar ta Quds, kamar yadda wakilan kungiyoyin Hamas da Jihadul Islami su za su gabatar da nasu bayanin.
Haka nan kuma daga cikin masu jawabin akwai Ibrahim Rasul gwamnan jihar Capetown, da kuma gwamnan jihar Johannesburg, da kuma wakilan kungiyoyin farar hula da masu kare hakkin bil adama daga kasashen duniya daban-daban.
Wannan shiri gudana ne a ranar 22 ga watan Mayu, wanda za a fara daga karfe 20:30 agogon Afirka ta kudu, kuma za a iya kallo da sauraren jawaban kai tsaye ta wanann adireshi na: Inestagram.com/sa.talk daga lokacin da aka fara.
Gwamnatin kasar Afrika ta kudu na daga cikin kasashen da suke kare hakkokin Falastinawa a matsayi na kasa da kasa, wanda hakan na daya daga cikin salon a siyasar da marigayi Nelson Mandela ya dora kasar a kansa.