IQNA

Bayanin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Kan Zagayowar Ranar Kafa Gwmnatin Sahyuniya

22:36 - May 14, 2020
Lambar Labari: 3484796
Tehran (IQNA) ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da bayani dangane da cikar shekaru 72 da kafa haramtacciyar gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Shafin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayar da bayanin cewa, yau ranar 14 ga watan Mayu aka cika shekaru 72 da kafa haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya a cikin Falastinu, wanda kuma tun daga lokacin ba a kara samun zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya ba har inda yau take.

Bayanin ya ce kafa gwamnatin yahudawan sahyuniya a cikin Falastinu da kuma yadda duniya ta yi gum da bakinta kan ta’asar da yahudawan suke aikatawa tsawon shekaru saba’in da biyu a akn al’ummar falastinu abin bakin ciki ne.

Kuma a cewar bayanin, shiru da gwamnatocin kasashen duniya suke yi kan hakan yana nuni da abubuwa guda biyu zuwa uku, ko dai akwai hadin bakinsu wajen cutar al’ummar falastinu da mamaye msuu kasa, ko kuma suna jin rauni da tsoro daga manyan masu girman kai na duniya, ko kuma ba su dalamiri na tausaya ma dan adam, akan haka suke nuna halin ko in kula da wannan batu.

Bayanin ya cea cikin wadanann shekaru fiye da saba’in, babu wani abu da aka gani daga yahudawan sahyuniya da suke yin hijira daga kasashen duniya Falastinu da sunan kafa kasar yahudawa, in ban da kisan kai da yake-yake da tayar fitina da haddasa husuma a tsakanin al’ummomin yankin.

Daga karshe bayanin ya yi ishara da cewa, dukkanin matsin lambar da kasar Iran take fuskanta daga manyan kasashe masu girman kai hakan an faruwa sakakon goyon baya da kare hakkokin al’ummar Falastinu da kasar ta Iran ke yi, amma kuma duk hakan Iran za ta ci gaba da yin tsayin daka domin kare hakkokin al’ummar Falastinu marassa kariya daga zaluncin da suke fuskanta.

 

3898846

 

 

 

captcha