IQNA

22:39 - May 14, 2020
Lambar Labari: 3484797
Tehran (IQNA) cibiyoyin Azhar da kuma Vatican sun kirayi al’ummomin duniya zuwa ga yin addu’oi na musamman a yau domin samun saukin cutar corona da ta addabi duniya.

Kwamitin hadin gwiwa tsakanin Azhar da Vatican ya sanar da cewa, yana kiran al’ummomin duniya da su ware ranar yau Alhamis domin yin addu’oi, domin samun sauki daga corona da kuma fatan ganin cutar kwaranye daga doron kasa.

Kwamitin ya ce a yau zai gabatar da bayani ta hanyar gizo kan addu’oin da kuma yadda ya kamata su kasance, musamamn ga mabiya addinin muslunci wadanda suke gudanar da azumin watan Ramadan, da kuma mabiya addinin kirista, da kuma sauran mabiya addinai.

Wannan kira ya samu karbuwa daga bangarori daban-daban na duniya, inda a nata bangaren kungiyar tarayyar Afrika ta bayyana hakan da cewa babban ci gaba ne, kamar yadda shugaban kungiyar na karba-karba kuma shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa, suna jaddada wannan kira ga dukkanin al’ummar Afirka.

Tun a shekara ta 2019 da ta gaba ce aka kafa kwamitin hadin gwiwa tsakanin cibiyar muslunci ta Azahar da ke kasar Masar, da kuma fadar Vatican ta mabiya addinin kirista, domin samar da zaman lafiya da fahimtar juna da taimakekeniya tsakanin mabiya addinan biyu a fadin duniya.

 

 

 

3898197

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: fadar vatican ، cibiyar azhar ، bayani ، hadin gwiwa ، mabiya addinai ، duniya ، musulmi ، kirista
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: