IQNA

Shirin Isra’ila Na Mamaye Yankunan Yammacin Kogin Jordan

23:33 - May 25, 2020
Lambar Labari: 3484835
Tehran (IQNA) firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa suna da shirin fara mamaye yankunan yamacin Kogin Jordan daga ranar 1 ga watan Yuli.

Kamfanin dillancin labaran Anadolu ya bayar da rahoton cewa, a wani zama da jam’iyyar Likud ta gudanar, shugaban jam’iyyar, kuma firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi furuci da cewa, suna da shirin fara mamaye yankunan yammacin Kogin Jordan daga ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa.

Ya ce suna daukar wannan yana daga cikin yarjejeniyar karni, kuma tun a shekara ta 1948 suke jiran damar da za su mamaye yankunan yammacin kogin Jordan, saboda haka yanzu dama ce ta zo, wadda ba za su taba bari ta kubuce musu ba.

A ranar 28 ga watan Janairun farkon wannan shekara ta 2020 ce dai shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya sanar da shirinsa na yarjejeniyar karni, tare shelanta birnin Quds a matsayin fadar mulkin Isra’ila.

Wannan shiri dai yana ci gaba da shan kakkausar suka da nuna rashin amincewa daga bangarori daban-daban na duniya, da hakan ya hada da majalisar dinkin duniya, da kuma kungiyar tarayyar turai gami da kungiyar tarayyar Afirka.

 

 

3901265

 

captcha