IQNA

23:56 - May 26, 2020
Lambar Labari: 3484838
Tehran (IQNA) shgaba Rauhani ya bukaci Switzerland ta kasance daga cikin masu bijirewa takunkuman Amurka.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar Iran Hassan Rohani ya yi da shugabar kasar Switzerland ya bayyana cewa Al’ummomin kasashen Switzerland da Iran suna da mahanga daya ta girmama juna, musamman a matsanancin halin da ake ciki na yaduwar Annobar cutar korona a kasashen duniya, amma takunkumin Amurka da ya sabama doka da matsin lambar tattalin arziki da take yi wa kasar Iran ya sake jefa Alummar kasar cikin mawuyacin hali.

Har ila yau shugaban yayi nuni game da muhimmancin kare yarjejeniyar da aka cimma kan shirin nukiliyar kasar Iran a matsayin yarjejniya ta kasa da kasa, ya nuna cewa yana da muhimmanci kungiyar tarayyar turai musamman kasashen turai 3 da su dauki da mataken da suka dace wajen ganin an ci gaba da aiki da yarjejniyar da aka cimma kan shirinta na Nukiliya, kuma kasar Swisland tana da muhimmiyar rawa da za ta taka wajen ganin yarjejeniyar ta kara karfi.

A nata bangaren shugabar kasar Switzerland ta nuna takaicinta game da ficewar Amurka daga yarjejeniya da aka cimma kan shirin nukiliyar Iran, kana ta jadda game da muhimmancin da ke tattare da kiyaye wannan yarjejeniya, don haka zata yi bakin kokarinta wajen ganin an ci gaba da kare yarjejeniyar kuma za ta karfafa sauran takwarorinta na kasashen turai wajen aiki da yarjejeniyar.

 

3901399

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Iran ، hassan rauhani ، shugaban kasar iran ، switzerland ، kasa da kasa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: