Kamfanindillancinlabaranreutersyabayardarahoton cewa, ma'aikatar kula da harkokin adini a yankin zirin Gaza na Falastinu ta bayar da umarnin bude masallatai a yankin.
Bayanin ya ci gaba da cewa,an dauki wannan matakin domin sassauta dokar takaita zirag-zirga da aka kafa ayankin domin dakile yaduwar cutar corona.
Yankin zirin Gaza dai yana killace tsawon shekaru masu yawa, inda al'mmar yankin kan fskanci matsaloli mas yawa a bangarori daban-daban da suka hada har da bangaren kiwon lafiya.
Bayanin ma'aikatar kula da harkokin addini ya kara da cewa, bayan sallali biyar babu wasu taruka da za a rika gudanarwa a cikin masallatai.