IQNA

23:52 - May 29, 2020
Lambar Labari: 3484847
Tehran (IQNA) Kungiyar kwatar ‘yancin Falastinawa ta PLO ta yi watsi da dukkanin yarjeniyoyin da ta rattaba a kansu tare da Isra’ila.

Falastinwa Sun Yi Watsi Da Dukkanin Yarjejeniyoyi Tsakaninsu Da Isra’ila

Kamfanin dillancin labaran Palestine ya bayar da rahoton cewa, a zaman fa kwamitin zartarwa na kungiyar PLO ya gudanar, ya sanar da yanke duk wata alaka, tare da dakatar da yin aiki da duk wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin Isra’ila da Falastinawa.

Kwamitin ya ce daukar wannan mataki na zuwa ne a matsayin martani kan shirin Isra’ila na mamayar yankunan Falastinawa na gabar yamma da kogin Jordan.

Bayanin ya ce, al’ummar Falastinu na bkatar ganin kasashen duniya sun sauke nauyin da ya rataya a kansu, na amincewa da kafa kasar Falastinu mai cin gishin kanta,a  kan iyakokin da majalisar dinkin duniya ta amince da su.

Kamar yadda kuma kwamtin ya kirayi manyan kasashe masu karfin fada a ji da s kirayi zama a majalaisar dinkin duniya, domin amincewa a hukmance da kasar Falastinu mai cin gishin kanta a kan iyakokin shekara ta 1967, wanda dokokin kasa da kasa suka amince da hakan.

 

 

 

 

 

3901715

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: