IQNA

Ana Samun Karuwar Talauci A Tsakanin Falastinawa

23:49 - June 01, 2020
Lambar Labari: 3484854
Tehran (IQNA) Bankin duniya ya bayar da wani rahoto da ke cewa, al’ummar falastinu na kara tsunduma a cikin matsanancin talauci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani rahoto da bankin duniya ya fitar a yau, ya bayyana cewa, sakamakon bincike da kwararru suka gudanar ya yi nuni da cewa, al’ummar falastinu na kara tsundum a cikin matsanancin talauci, sanadiyyar bullar cutar corona.

Rahoton ya ce, tun kafin bullar cutar corona, akwai talauci a dukkanin bangarori biyu na falastinu, da hakan ya hada da yankunan Yammacin kogin Jordan, da kuma zirin Gaza, inda adadin masu fama da talauci a yankunan yammacin kogin Jordan ya kai kashi 14 cikin dari, a Gaza kuma ya kai kashi 53 cikin dari.

Bayanin ya ce bayan bullar cutar corona, sakamakon killace jama’a da kuma karuwar rashin ayyukan yi, adadin yana ci gaba da karuwa, inda ake ganin a yankunan yammacin kogin Jordan, adadin Falastinawa da suka fada cikin matsanancin talauci zai iya kaiwa kasha 30 cikin dari, a gaza kuma zai iya kaiwa kasha 63 cikin dari.

Haka nan kuma bayanin na bankin duniya ya yi ishara da cewa, baya ga matsalar corona, kudaden shiga da gwamnatin Falastinawa take samu sun ragu matuka a cikin lokutan baya-bayan nan.

 

 

3902360

 

captcha