IQNA

23:53 - June 08, 2020
Lambar Labari: 3484874
Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya aike da sakon ta’aziyyar rasuwar tsohon babban sakataren kungiyar fafutuka ta Falastinawa Jihadul Islami Dr. Ramadan Abadullah Shalah.

Shafin yanar gizo na shugaban kasar Iran ya bayar da bayanin cewa, a yau ne shugaban ya fitar da wani bayani da a cikinsa yake yin ta’aziyya ga al’ummar Falastinu, kan rasuwar Dr. Shalah.

Matanin sakon shugaba Rauhani kamar haka:

Bayan faraway da sunan Allah mai rahma mai jin kai

Shugaban ya yi ishara da cewa, rashin Dr. Ramadan Shalah babban rashi ne ga al’ummar Falastinu da ma dukkanin al’ummomin musulmi da ma masu lamiri na duniya.

Ya ce Dr. Abdullah Shalah jagora ne da ya sadaukar da dukkanin rayuwarsa da lokacinsa domin hidima ga al’ummarsa ta Falastinu, wanda tarihin gwagwarmayar Falastinawa ba zai manta da shi ba.

Haka nan kuma ya isar da sakon ta’aziyya ga dukkanin al’ummar Falastinu da kuma dangi da iyalansa da sauran makusantansa, tare da yi masa addu’ar neman samun gafara da rahamar Allah.

 

3903562

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: