IQNA

22:57 - June 15, 2020
Lambar Labari: 3484898
Tehran (IQNA) kungiyar larabawan Yemen 'yan kabilar Huthi masu gwagwarmaya da 'yan mamaya a kasar sun bayyana shirinsu na tattaunawa da Saudiyya.

Shugaban majalisar koli da juyin huya hali a Yemen Muhammad Ali Alhuthi ya bayyana cewa, a shirye suke su yi tattaunawa ta  gaba da gaba kuma a bayyane tare da Saudiyya, domin kawo karshen yakin da take yi da al’ummar Yemen.

A zantawarsa da tshar talabijin ta BBC bangaren larabci,  Shugaban majalisar koli da juyin huya hali a Yemen Muhammad Ali Alhuthi ya tabbatar da cewa, ba su da wata matsala kan tattaunawa da Saudiyya, abin da yake da muhimamnci shi ne ta aiwatar da abin da aka cimmawa na dakatar da yaki a kan al’ummar kasar Yemen.

Ya ce a kowane lokaci gwamnatin Saudiyya tana tuntubarsu ta bayan fage domin cimma matsaya kan yin sulhu da kuma kawo karshen yaki a Yemen, amma kuma ba ta aiwatar da duk abin da aka cimmawa, maimakon hakan ma sai ta kara zafafa hare-haren nata a kan al’ummar Yemen.

Alhuthi ya ce a yanzu haka akwai manyan jiragen ruwa na daukar makamashi guda 15 da suke dauke da makamshi zuwa yemen, wadanda Saudiyya ta tsare a  cikin ruwa, kuma ta hana su kai makamashin zuwa Yemen.

Dangane da batun corona kuwa, Alhuthi ya bayyana cewa, cutar tana ci gaba da bzuwa a tsakanin jama’a, a daidai lokacin da kasashen da suke yaki da kasar suke ci gaba da killace ta, tare da hana shigar da duk wani abin da zai taimaka wajen yaki da corona a kasar.

3904910

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: