IQNA

21:15 - June 17, 2020
Lambar Labari: 3484903
Tehran (IQNA) Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa suna da martani mai hatsari da za su mayar matukar aka nemi jefa Lebanon cikin rashin abinci.

Babban magatakardar kungiyar Hizabullah ta Lebanon ya bayyana cewa; suna da martani mai hatsari da za su mayar wanda kuma ba za su bayyana shi ba a yanzu, matukar aka nemi jefa kasar cikin rashin abinci da yunwa.

Sayyid Nasarllah wanda ya gabatar da jawabi a daren Talata ya ci gaba da cewa; Abinda Amurkawa suke nema a cikin Lebanon shi ne yadda za su kare manufofin Isra’ila da tsaron Isra’ila akan iyakokin kasa da na ruwa, kuma ba abinda ya hada su da kare hurumi ko manufar Lebanon, ba kuma kaunar al’ummar Lebanon din su ke yi ba, Isra’ila da manufofinta ne kawai a gabansu.”

Jagoran kungiyar ta kungiyar Hizabullah ya kara da cewa; Wadanda su ka dogara da cewa za mu fada cikin yunwa, su saurara su ji, ba za fada cikin yunwa ba, ba kuma za mu bari Lebanon ya fuskanci yunwa ba.”

Har ila yau, Sayyid Nasarallah ya ce; Ba za mu mika kai ga Amurka ba,yunwa ba za ta sa mu rusuna a gabanku ba.”

Sayyid Nasarllah ya bude jawabinsa da mika ta’aziyyar shahadar Imam Ja’afar Assadiq ( a.s) zuwa ga al’ummar musulmin duniya. Bugu da kari, ya yi ta’aziyyar rasuwar Dr. Abdullah Shalah, tsohon magatakardan kungiyar Jihadul-Islami tare da yin ishara da tarihinsa na son hada kan kungiyoyin Palasdinawa da kuma al’ummar musulmi.

 

 

3905366

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: