IQNA

Mutane 15 Ne Suka Mutu Ko  Jikkata Bayan  Tarwatsewar Wani Abu A Makarantar Kur’ani A Afghanistan

22:59 - June 18, 2020
Lambar Labari: 3484906
Tehran (IQNA) wani abu da ya tarwatse a cikin wata makaranta a kasar Afghanistan ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkatar mutane.

Tashar euro news ta bayar da rahoton cewa,a  yau wani abu mai karfi ya tarwatse a cikin wata makaranta a yankin Takhar a kasar Afghanistan.

Rahoton ya cea n tabbatar da mutuwar mutane tara da kuma jikkatar shida, amma babu cikakken bayani kan hakikanin abin da ya faru.

Wasu bayanan sun ce wasu manyan harsasai ne a ka ajiye a cikin makarantar wadanda suka tarwatse, kuma suka kashe daliban ad suke a wurin.

Wasu bayanan kuma na cewa akwai yiwuwar an harba makamin roka ne wanda ya sauka a cikin makarantar, kuma ya tarwatsa wani bangaren gininta tare da kashe mutane.

A halin yanzu jami’an tsaro suna gudanar da bincike kan hakikanin abin da ya faru kafin dora alhakin hakan a kan wani bangare.

 

3905542

 

Abubuwan Da Ya Shafa: abin da ya faru ، kafin ، dora alhakin ، wani bangare ، sauka ، makarantar ، Afghanistan
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :