IQNA

23:55 - June 20, 2020
Lambar Labari: 3484911
Tehran (IQNA) ana shirin gudanar da wani gagarumin gangamia kasar Switzerland domin nuna rashin amincewa da shirin yarjejeniyar karni.

Ana shirin gudanar da wani gagarumin gangami a kasar Switzerland domin nuna  rashin amincewa da shirin yarjejeniyar karni, da kuma shirin mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan.

Wannan jerin gwano zai fara ne daga misalin karfe 14 wato biyu na rana a yau Lahadi agogon kasar ta Switzerland, tare da halartar jama'a daban-daban.

Daga cikin wadanda za su halarci wannan gangami akwai malaman jami'oi da kuma kungiyoyin farar hula masu zaman kansu, kamar yadda kungiyoyin larabawa da na musulmi a kasar ma za su shiga wannan gangami.

Babbar manufar hakan dai ita ce fadakar da mutanen nahiyar turai halin da ake ciki na yunkurin kammala mamaye sauran yankunan Falastinawa da suka rage, wanda Isra'ila take shirin aiwatarwa.

Wannan sihiri dai yana fukskantar kakkausar suka daga bangarori daban-daban a duniya har da kasashen nahiyar turai.

 

 

 

3905716

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: