IQNA

Ita dai jikar manzon Allah ce, an haife ta a Madina ta samu tarbiya da ilmi a wajen mahaifinta, sannan bayan shahadarsa ta koma karkashin renon. Sai kuma bayan da sarki Ma'amun daga cikin sarakunan Abbasiyawa ya tilasta wa yayanta yin hijira zuwa Maru a yankin Khurasan, ta fito daga Madina domin ziyartarsa, amma sai rashin lafiya ta kama ta a kan hanya. sannan bayan kwanaki sha bakawai da jinya ta rasu a birnin qum a rana irin ta yau a shekara ta dari biyu da daya hijira kamariyya.