IQNA

23:23 - June 23, 2020
Lambar Labari: 3484919
Tehran (IQNA) kakakin rundunar sojin Yemen a gwamnatin San’a ya ce sun mayar da martani da makamai masu linzami kan hare-haren Al saud a kan kasarsu.

Yan gwagwarmayar neman sauyi na Ansarullah, a kasar Yemen, sun kai wasu jerin hare haren makamai masu linzami na maida martani kan yakin da Saudiyya ke ci gaba da jagoranta a kasar yau sama da shekaru biyar.

Gidan talabijin na al-Masirah, dake da kusanci da ‘yan kungiyar ta Ansarullah, ya tabbatar da kai harin, tana mai cewa nan gaba kakain rundinar sojin kasar Birgediya Janar, Yahya Saree, zai yi karin bayyani.

Shi ma da yake tabbatar da hakan kawancen yakin da Saudiyya ke jagoranta a Yemen, ya ce an kai hare hare kan biranen Riyad, Najran da Jiza, saidai an murkushe hare haren.

Kakakin kawancen Kanal, Turki al-Malki, ya yi tir da harin wanda aka kai kan fararen da kuma dukuyoyinsu.

 

 

3906467

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ansarullah ، kasar yemen ، harin martani ، kan Saudiyya ، jagoranta ، gwamnati
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: