IQNA

Karamin Yaro Mai Fansar Da Kur’ani A Masar Da Ya Nuna Hali Abin Koyi

22:57 - July 05, 2020
Lambar Labari: 3484953
Tehran (IQNA) Muhammad dan shekaru 10 da haihuwa daga yankin Muhandisin a kasar Masar ya nuna wani hali mai wanda yake abin koyi ko ga manya.

Jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da wani yaro mai fansar da kur’ani mai tsarki yake kan titi domin neman halal dinsa, ya nuna wani kyakkyawan hali da ya baiwa kowa mamaki.

Rahoton ya ce a lokacin da yaron mai suna Muhammad yake tsaye gefen titi yana fansar da kur’ani, a garin Muhandisin da ke cikin gundumar Jiza a kasar Masar, wani matashi dan kasar Libya ya ba shi kyautar kudi har fan dubu daya na kasar Masar, amma yaron yaki karba.

A lokacin da ya tambaye shi dalilin hakan, sai yaron ya ce saboda yana sayar da kur’ani , kuma ba zai yi bara da littafin Allah da ke dauke da zancen Allah ba, saboda haka yak an karbi kudi ne idan an sayi kur’ani a wurinsa domin hakan shi ne halas dinsa.

Jaridar Yaum sabi ta ce lamarin ya faru ne a daidai lokacin da dan rahotonta yake daukar hoton wannan yaro da wayar salula, kuma ta yada wannan hoto domin ya zama darasi abin koyi daga kyawawan halaye da hotodabiu na wannan yaro.

3908566

 

Abubuwan Da Ya Shafa: darasi ، abin koyi ، kyawawan halaye ، hoto ، matashi ، gefen
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha