IQNA

Wakilin Iran A MDD: Shahid Sulaimani Abin Alfahari Ne Ga Al’umma

23:50 - July 09, 2020
Lambar Labari: 3484967
Tehran (IQNA) wakilin Iran a majalisar dinkin duniya ya bayyana Shahid Qasem Sulaimani da cewa abin alfahari ne ga al’umma.

Shafin yada labaran na ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayar da rahoton cewa, Isama’il Baghaei Hamaneh wakilin Iran a majalisar dinkin duniya ya bayyana Shahid Qasem Sulaimani da cewa abin alfahari ne ga al’umma baki daya gami da ‘yantattu na duniya.

Ya bayyana hakan ne a zaman da aka gudanar a kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya, inda aka mika sakamakon bincike kan kisan Qasem Sulaimani da gwamnatin kasar Amurka ta yi a farkon wannan shekara a cikin kasar Iraki tare da mataimakin babban kwamandan dakarun sa kai na kasar.

Babbar jami'ar da ke bincike kan kisan gilla ta Majalisar Dinkin Duniya Agnes Calamard ta bayyana cewa kisan da Amurka ta yi wa babban kwamandan Sojin Iran a ketare Janar Qasem Soleimani, ya saba wa dokokin kasa da kasa.

Jami’ar ta ce, kisan Janar Shahid Qasem Soleimani na Iran abu ne da ya saba wa doka da kuma muradun majalisar, tana mai kara da cewa babu wata kwakwarar shaidar da Amurka ta bayar, da ke nuni da cewa akwai shirin kai ma ta hari.

Rahoton dai na abunda jami’ar ta gano ne, ba wai na majalisar dinkin duniya  ba ne, a yau ne ranar yau ne ta gabatar da rahoton a taron hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar a Geneva.

 

3909628

 

 

captcha