IQNA

Cibiyar Agaji Ta Musulmin Amurka Za Ta Taimaka Ma Al’ummar Yemen

23:22 - July 10, 2020
Lambar Labari: 3484971
Tehran (IQNA) cibiyar agaji ta musulmin kasar Amurka za a ta taimaka al’ummar Yemen da kayan abinci da magunguna da zai kan dala miliyan goma.

Shafin yada labarai an Yemen Online ya bayar da rahoton cewa, cibiyar agaji ta musulmin kasar Amurka Islamic Relief za a ta taimaka al’ummar Yemen da kayan abinci da magunguna da zai kan dala miliyan 10 a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Rahoton ya ce, cibiyar za ta ware wadannan kudaden ne daga cikin kudadenta da take gudanar da ayyuka duk da matsalar karancin kudi da cibiyar ke fama da shi, amma bisa la’akari matsanancin halin da aka jefa al’ummar kasar, hakan yasa cibiyar yanke shawarar daukar wannan mataki.

Taimakon dai zai kunshi kayan abinci da kuma magunguna, wanda mutane kusan miliyan biyu da rabi ne za su taimakon a kasar ta Yemen.

Kungiyar bayar da agaji ta majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa akwai bukatar kudade kimanin dala biliyan biyu da rabi domin kai daukin gagawa ga al’ummar Yemen da suke cikin mawuyacin hali, sakamakon yakin da wasu kasasashe suke kaddamarwa kan al’ummar kasar, amma har yanzu ba a iya tara wani abin azo a gani ba.

 

3909662

 

Abubuwan Da Ya Shafa: har yanzu ، mawuyacin hali ، gagawa ، kaddamarwa ، bukatar ، kudade
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha