IQNA

Saudiyya ta Kashe Fararen Hula 25 A Yemen

19:26 - July 16, 2020
Lambar Labari: 3484991
Tehran (IWNA) Mutane Da Dama Da Su Ka Hada Mata Da Kananan Yara Sun Yi Shahada Sanadiyyar Hare-haren Saudiyya

Tashar talabijin din almasirah ta kasar Yemen ta ce harin da jiragen yakin abokan gabar su ka kai a yankin Jauf da safiyar yau Laraba, ya yi sanadin shahadar fararen hula da mafi yawancinsu mata ne da kananan yara, bayan rusa gidaje uku.

Tashar talabijin din ta ci gaba da cewa; Jami’an agaji suna kokarin fito da gawawwakin mutanen daga cikin baraguzai.

A ranar Lahadin da ta gabata ma dai jiragen yakin na Saudiyya sun kai wasu hare-haren a yankiin Washha da ke gundumar Hijjah, tare da kashe mutane 9 dukkaninsu mata da kananan yara, da kuma jikkata wasu mutane biyu.

Yakin da Saudiyya ta shelanta akan kasar Yemen ya shiga cikin shekara ta shida, kuma ya zuwa yanzu ya ci dubban rayuka da kuma jikkata wasu dubun dubata.

 

3910818

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha