IQNA

Martanin Iran Kan Hare-Haren Da Jiragen Yakin Saudiyya Suka Kaddamar A Yemen

20:59 - July 17, 2020
Lambar Labari: 3484993
Tehran (IQNA) Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Musawi ya yi tir da Allawadai da hare-haren Saudiyya a kasar Yemen.

A cikin wani bayani da ya fitar a yau Juma’a, Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Musawi ya bayyana cewa, babban abin takaici ne yadda rayukan fararen hula mata da kananan yara a Yemen suka zama a kansu ne ake gwada makaman da aka saya a hannun turawa.

Ya ce abu mafi muni kuma abin kunya shi ne, yadda ya zama masu kai hare-haren kan kananan yara da mata tare da yi musu kisan gilla gwamnatocin da ke ikirarin musulunci ne, baya ga haka kuma makwafta na tarihi ga al’ummar Yemen baya ga ‘yan uwantaka ta musulunci.

Haka nan kuma Musawi ya caccaki kasashen turai masu da’awar bin tafarkin demokradiyya da kare hakkin bil adama a duniya, wadanda suke da hannu kai tsayea  cikin wannan ta’asa, baya ga haka kuma su ne kan gaba wajen sayar da wadannan makamai ga masarautar Al saud da take yin lugudansu a kan fararen hula musulmi a kasar Yemen.

Daga karshe Musawi ya kirayi majalisar dinkin duniya da sauran manyan kasashen duniya masu fada a ji das u sauke nauyin day a rataya  akansu wajen kawo karshen wannan rashin imani da rashin ‘yan adamtaka da kuma abin kunya mafi muni a duniya.

3910967

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iran hare-haren saudiyya yemen mata kananan yara
captcha