IQNA

An Dauki Kwararan Matakai Domin Aikin Hajjin Bana

17:51 - July 20, 2020
Lambar Labari: 3485001
Mahukunta a kasar Saudiyya sun dauki kwararn matakai domin gudanar da aikin hajjin bana.

Shafin yada labarai Ajel ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Saudiyya ta sanar da sabbin matakan kariya ga wadanda za su gudanar da aikin hajjin bana.

Daga matakan hard a bayar da umarni ga dukkanin wadanda aka yi wa rijistar gudanar da aikin hajjin bana da suke a cikin kasar a halin yanzu, da su killace kansu na tsawon kwanaki bakawai kafin su nufi Makka, wanda hakan ya fara tun daga ranar Asabar da gataba.

Sannan kuma za su isa Makka a ranar uku ga watan Zul hijjah, inda  a can ma za a sake killace su a Makka na tsawon kwanaki hudu.

A lokacin killace su za a sake yi musu gwaje-gwaje kafin ranar da za su fara aikin hajji, sannan kuma dukkanin harkokinsu za su kasance a cikin kulawa ta musamman ta jami’an kion lafiya.

Rahoton ya ce baya ga matakai na bayar da tazara da kuma saka takunkumin fuska da sauran matakai na kariya, duk mutane 20 za a sanya musu  jami’in kiwon lafiya guda da zai sanya ido a kansu da kuma kula da yadda suke kiyaye matakan kariya,

Wadannan matakai za su ci gaba har zuwa lokacin da za a kammala aikin hajjin wanda mutanen da aka yi rijista ne kawai za a baiwa damar gudanar da shi.

 

3911338

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: makka ، hajjin bana ، mutane ، matakai ، kiwon lafiya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha