IQNA

An Bude Rijistar Daukar Malaman Kur’ani Domin Koyar da Yara A Masar

22:32 - July 24, 2020
Lambar Labari: 3485014
Tehran (IQNA) an bude rijistar daukar malaman kur’ani a kasar Masar domin koyar da kananan yara.

Jaridar yau sabi ta bayar da rahoton cewa, a jiya ma’ikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta sanar da cewa, an bude rijistar daukar malaman kur’ani a kasar domin koyar da kananan yara a makarantun kur’ani.

Wannan shiri dai zai shafi makarantun da ake koyar da kur’ani da kuma ilmomin addini ne, kamar yadda kuma malamai masu shedar karatun kr’ani ko na addini ne za a dauka domin wannan aiki.

Bayanin ya ce limamai da suka samu horo karkashin ma’ikatar kula da da harkokin addini, wadanda su ne kan gaba wajen aiwatar da wanann shiri, kamar yadda kuma su ne za su tantance dukkanin malaman da za a dauka domin koyar da yara karatun kur’ani a fadin kasar.

 

3912154

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: tantance ، malaman ، fadin kasar ، harkokin addini ، masar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha