IQNA

Taho Mu Gama Tsakanin Falastinawa Da Yahawan Isra'ila

23:55 - July 25, 2020
Lambar Labari: 3485021
Tehran (IQNA) yahudawa sun yi amfani da karfi kan falastinawa masu jerin gwanon lumana.

Tashar alalam ta bayar rahoton cewa, yan sandan Sahayoniya sun yi amfani da karfi akan samarin na garin Kafar-Kudum da su ka saba yin gangami a kowane mako domin yin tir da mamaya, da kuma bukatar da a bude titin garin nasu da aka rufe tun shekaru 16 da su ka gabata.

Har ila yau samarin palasdinawan sun yi tir da shirin ‘yan sahayoniya na shimfida iko da yankin yammacin kogin Jordan.

Kakakin gwagwarmayar ruwan sanyi a yakin Qalqeliya Murad Shatitu ya tabbatar da jikkata samarin hudu bayan da aka harbe su da harsashin roba. Har ila yau, ‘yan sahayoniyar sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye akan masu gangamin da ya haddasa shakewar gwammai daga cikinsu.

 

3912526

 

Abubuwan Da Ya Shafa: yahudawan sahyuniya ، amfani ، karfi ، falastinawa ، jerin gwano
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha