IQNA

Hizbullah Ta Ce Yahudawan Sahyuniya Su Saurari Martani

21:58 - July 27, 2020
Lambar Labari: 3485028
Tehran (IQNA)n kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa harbe-harben da aka ji daga bangaren makiya ne.

Tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, kungiyar Hizbullah ta sanar da cewa, makiya ne suka fara kaddamar da harin, kuma harbe-harben da aka yi ta ji daga bangaren makiya ne, domin su ne matsorata da suke cikin damuwa da zullumi.

Isra'ila dai tana cikin damuwa, tun bayan kisan Ali Muhsin Kamil daya daga cikin dakarun kungiyar Hizbullah ta yi a cikin wannan mako a kasar Syria.

Haka nan Isra’ila ta yi ta kamun kafa da Majalisar dinkin duniya da kuma kasar Rasha, kan su sanar da Hizbullah cewa bisa kure ne hakan ta faru ba da niyya ba, kuma su tausasa Hizbullah domin kada ta mayar da martani.

Haka an kuma bayanin da Hizbullah ta fitar a yau ya jaddada cewa, harin martani da ramuwar gayya kan kisan Ali Muhsin Kamil na nan zuwa.

3912993

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: hizbullah ، lebanon ، ramuwar gayya ، martani ، yahudawan sahyuniya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha