IQNA

Haniyya Da Abbas Sun Jaddada Wajabcin Hadin Kan Al’ummar Falastinu

14:22 - July 31, 2020
Lambar Labari: 3485040
Tehran (IQNA) shugaban Falastinawa Mahmud Abbad da shugaban Hamas Isma’il Haniyya, sun jadadda wajabcin hada kan al’ummar falastinu.

A cikin wani bayani da kungiyar Hamas ta fitar, ta sanar da cewa; an gudanar da wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Haniyya da Abbas, inda suka jadadda wajabcin hada kan al’ummar falastinu domin tunkarar kalubalen da ke a gabansu.

Daga cikin muhimman abubuwan da suka tattauna akwai batun shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastina da ke yammacin kogin Jordan, da kuma batun birnin Quds.

Bangarorin biyu sun jaddada cewa dole ne dukkanin bangarorin al’ummar Falastinu su hada kai domin tunkarar wannan kalubale, tare da tabbatar da cewa sun fifita maslahar kasa da al’umma a kan maslaha ta daidaiku.

 

3913744

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Hamas ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha