IQNA

21:31 - August 03, 2020
Lambar Labari: 3485051
Tehran (IQNA) cibiyar musulmi da ke birnin New York na kasar Amurka ta bude gwajin cutar corona kyauta ga dukkanin mutane.

Shafin The West Bury Times ya bayar da rahoton cewa, a yau an bude gwajin cutar corona kyauta ga dukkanin mutane a babban ginin cibiyar musulmi da masallaci da ke birnin New York na kasar Amurka wato Islamic Center of Long Island, daga nan har zuwa ranar Juma’a mai zuwa.

Bayanin cibiyar ya ce, ana kira ga mutanen da suke bukatar yin gwaji kan cutar corona da su zo wanann masallaci da cibiya ta musulmi domin yin gwaji kyauta, kuma ana karfafa gwiwar mutane da su gwajin domin sanin hakikanin wadanda suke da cutar a wannan birni.

Ya zuwa yanzu sama da mutane dubu 32 ne cutar corona ta lakume rayukansu a birnin na New York.

3914348

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: