IQNA

14:42 - August 04, 2020
Lambar Labari: 3485053
Tehran (IQNA) a karon farko an yi amfani da tufafin Ihrami da aka samar daga fasahar Nanu a aikin hajjin bana.

Jaridar Ukaz ta kasar Saudiyya ta bayar da rahoton cewa, a a karon farko an yi amfani da tufafin Ihrami da aka samar daga fasahar Nanu a aikin hajjin bana wanda yake bayar da kariya daga kamuwa da kwayoyin cuta.

Ahmad Alyami wani masani ne dan kasar Saudiyya wanda kuma ya samar da wannan tufafi a karon farko a bangaren ayyukan masaku na kasar ta Saudiyya, wanda aka yi amfani da shi a aikin hajjin bana.

Wannan tufafi dai an samar da shi ne daga auduga zalla, kuma za  aiya wanke shi har sau 90 ba tare da ya samu wata matsala, kuma yana da sanadarai na kariya a tattare da shi.

 

3914577

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Nanu ، tufafi ، ihrami ، aikin hajjin bana ، alhazai ، masaku ، Saudiyya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: