IQNA

21:27 - August 06, 2020
Lambar Labari: 3485061
Tehran (IQNA) babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Ozma Sayyid Ali Sistani ya mika sakon ta’aziyya ga al’ummar kasar Lebanon, biyo bayan mummunan hatsarin da ya faru a birnin Beirut .

A cikin bayanin da ofishinsa da ke birnin Najaf ya fitar a yau, Babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Ozma Sayyid Ali Sistani, bayan mika sakon ta’aziyya ga al’ummar kasar Lebanon, ya bayyana abin da ya auku a birnin Beirut da cewa lamari ne mai matukar sosa rai da sanya damuwa matuka.

Ya ce wannan babbar jarabawa ce wadda take bukatar hakuri da juriya, da kuma mayar da lamurra ga Allah madaukakin sarki, wanda shi babban mai taimako ga adam a cikin dukkanin mawuyacin halin da ya samu kansa a ciki.

Haka nan kuma Ayatollah Ozma Sistani ya yi kira ga dukkanin al’ummar musulmi da su kasance a sahun gaba wajen taimaka ma ‘yan uwansu a kasar Lebanon a cikin wannan mawuyacin hali.

A nasu bangaren dakarun sa kai na al’ummar Iraki na Hash Al-sha’abi, tuni suka fara taimako na kudade da kayayyakin buakat rayuwa, domin aikewa ga wadanda wannan ibtila’i ya shafa a kasar ta Lebanon.

 

3915092

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: