IQNA

22:24 - August 07, 2020
Lambar Labari: 3485064
Tehran (IQNA) babban jirgin daukar kayayyaki na uku na kasar Iran ya isa birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon dauke da kayan agaji zuwa ga al’ummar kasar.

Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, a daren jiya jirgin na uku na kasar Iran da ke dauke da kayan agaji zuwa ga al’ummar Lebanon da ibtila’i ya shafa ya isa birnin Beirut fadar mulkin kasar.

Mataimakin shugaban hukumar bayar da agajin gaggauwa ta kasar Iran Muhammad Baqir Muhammadi ya bayyana cewa, jirgin na uku na yana dauke ne da wasu magunguna na musamman, da suka hada da magungunan kunar wuta, da kayan aikin dori ga wadanda suka samu karayar kasusuwa a cikin jikinsu.

Ya kara da cewa, Iran za ta ci gaba da aikewa da dukkanin kayayyakin da ake bukata zuwa kasar ta Lebanon domin taimaka ma wadanda lamarin ya shafa.

A daya bangaren gwamnatin Lebanon ta sanar da cewa, a yau Juma’a kayayyakin taimako na kasar Iraki za su isa kasar ta Lebanon, inda gwamnatin Iraki ta sanar da cewa za ta aike da kayan abinci musamman alkama zuwa kasar ta Lebanon domin rabawa ga jama’a.

 

3915165

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: