Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Shauki Allam babban mufti na kasar ya bayar da fatawa a kan hukuncin renon kare a cikin gida, halascinsa ko akasin haka.
A cikin jawabin da ya bayar, shehin malamin ya bayyana cewa, akwai sabanin ra’ayoyi tsakanin malamai a kan wannan mas’ala, inda dukkanin mazhabobina ‘yan sunnah suka tafi akan cewa kare najasa ne.
Ya ce amma bisa mazhabar Malikiyya wadda akanta yake bayar da fatawa kare ba najasa ba ne.
Wannan fatawa ta bar baya da kura, inda jama’a da dama suke ci gaba da mayar da martani a kan haka, tare da bayyana cewa koa mazhabar malikiyya ruwan jikin kare ko yawunsa najasa ne.