IQNA

21:56 - August 19, 2020
1
Lambar Labari: 3485103
Tehran (IQNA) daya daga cikin ‘yan sandan birnin Dubai na kasar UAE ta yi murabus daga aikinta saboda kasar ta kulla alaka da Isra’ila.

Shafin yada labarai na skywaterjo ya bayar da rahoton cewa, rana Ibrahim Katibah, daya daga cikin jami’an ‘yan sanda na birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa

wadda asalinta bafalastiniya ce ta yi murabus daga aikinta saboda kasar ta kulla alaka da gwamnatin yahudawa.

A cikin takardar da ta rubuta wa babban kwamishinan ‘yan sanda na birin Dubai, Rana ta bayyana cewa a matsayinta na balaraba musulma mai kishin addininta da kabilarta, ba za ta taba yin aiki da duk wata da ta kulla alaka da kawance da haramtacciyar kasar Isra’ila ba, wadda ta mamaye musu kasa bisa zalunci.

A kan haka ta ce ta yi murabus daga aikinta a matsayinta na ‘yar sanda a kasar hadaddiyar daular larabawa, saboda wannan kasa ta mika kai wajen kulla alaka da yahudawa wanda hakan ita ya sabawa imaninta da akidarta.

Ta kara da cewa hatta shedar zama dan kasa da aka bata a UAE ba ta da bukata, kuma bata da bukatar kudin sallama daga aiki, ta ce ta bayar da wadannan kudin kyauta ga cibiyoyin da suke gudanar da ayyukan taimako ga mabukata.

 

 

3917512

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: hadaddiyar daular larabawa ، kulla alaka ، murabus ، aiki ، birnin Dubai
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Shafiu sunusi
0
0
Tabbas wannan baiwar Allah tayi abinda ya dace A matsayinta na musulma kuma ta nunawa duniya cewa musulmi bashi da kwadayi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: