IQNA

22:09 - August 19, 2020
Lambar Labari: 3485104
Tehran (IQNA) sakon ta’aziyyar rasuwar babban sakataren kwamitin koli na cibiyar kusanto da mazhabaobin muslunci na duniya Ayatollah Taskhiri daga Jagoran juyin juya halin muslunci na kasar Iran.

A cikin bayanin da jagoran ya fitar a jiya, ya bayyana rashin Sheikh Muhammad Taskhiri da cewa babban rashi ne na al’umma baki daya, kasantuwarsa mutum ne da rayuwarsa da lokacinsa baki daya domin hidima ga addinin musulunci.

Baya ga haka kuma jagoran ya bayyana irin gudunmawarsa da shehin malamin ya bayar wajen ganin an karfafa hadin kan al’ummar musulmi a duniya da cewa, aiki ne wanda ba za a taba mantawa da shi ba.

A jiya ne Allah ya yi wa Ayatollah Muhammad Ali Taskhiri rasuwa a birnin Tehran, bayan fama da rashin lafiya.

Cibiyoyi da kungiyoyin musulmi da manyan malamai daga sasa daban-daban na duniya suna ci gaba da aikewa da sakonnin ta’aziyyar rasuwarsa, ga jagoran juyin juya halin muslunci na Iran da kuma iyalansa da sauran makusantansa.

 

3917395

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: