IQNA

Zanga-Zangar Allawadai Da UAE A Tunisia Kan Kulla Alaka Da Isra’ila

22:49 - August 23, 2020
Lambar Labari: 3485114
Tehran (IQNA) mutanen birnin Tunis a kasar Tunisia sun gudanar da gangami na yin tir da UAE kan kulla alaka da ta yi da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a yau jama’a sun fito a cikin birnin Tunis fadar mulkin kasar Tunisia suna gudanar da gangami na yin tir da gwamnatin kasar UAE kan kulla alaka da ta yi da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Masu gangamin da jerin gwano sun data tutocin Falastinu, suna rera taken cewa rayukansu yana a matsayin sadaukarwa ga masallacin Quds da alfarmarsa.

Bashir Alkhazri shugaban kungiyar taimakon falastinawa a Tunisia ya bayyana a wajen jerin gwanon cewa, abin da UAE ta yi cin amana ne ga dukkanin al’ummomin musulmi da na larabawa.

Khaula Alubaidi daya daga cikin mata masu fafutuka  akasar ta Tunisia ta bayyana cewa,a  cikin wannan makon za su ci gaba da gudanar da taruka na nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu, da kuma yin tir da masu ha’intar falastinu daga cikin larabawa.

3918358

 

 

 

 

 

captcha