IQNA

22:45 - August 26, 2020
Lambar Labari: 3485122
Thran (IQNA) ministan ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar ya bayyana cewa haram ne mutumin da yasan yana dauke da corona ya yi salla a cikin masallaci.

Shafin yada labarai na al’ain ya bayar da rahoton cewa, Muhammad Mukhtar Juma’a ministan ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar ya bayyana cewa haram ne mutumin da yasan yana dauke da corona ya yi salla a cikin masallaci tare da jama’a ko shi kadai.

Ya ce a lokacin da aka samu kawo karshen wanann cuta kowa yana da hurumin ya shiga masallaci ya yi amma a irin wanann yanayi da ake ciki wanda ya san yana dauke da wannan cuta haram ne a aknsa a cikin masallaci domin wasu za asu iya dauka.

Mukhtar Juma’a ya ce, a cikin wannans hekara ta 2020 zuwa 2021 an ware kudade da suka kai fan na kasar Masar miliyan 677 domin daukar nauyin limamai a kasar.

 

3918570

 

 

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: