Shafin jagora ya bayar da rahoton cewa, a daren jiya jagora ya halarci zaman juyayin Muharram a Husainiyar Imam Khomenei (RA) amma ba tare da halartar jama’a ba kamar yadda aka saba yi a kowace shekara, saboda kiyaye kaidoji an kiwon lafiya.
Hojjatol Islam Siddiqi shi ne ya gabatar da bayani, tare da ambatar muhimman lamurra da suka waka a irin wannan rana a lokacin da Imam Hussain (S) tare da iyalan gidan manzon Allah suke kan hanyar isa Karbala.