IQNA

19:28 - August 28, 2020
Lambar Labari: 3485128
Tehran (IQNA) da dama daga cikin jam’iyyun siyasa kasar Sudan sun gargadi gwamnatin kasar kan yunkurin kulla alaka da Isra’ila.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa,jam’iyyun siasa na kasar Sudan sun fitar da bayanai na hadin gwiwa inda suke gargadi gwamnatin kasar kan yunkurin kulla alaka da Isra’ila.

Bayanin jam’iyyun siyasar na kasar Sudan ya mayar da hankali ne kan irin hadarin da yake tatatre da mataki da gwamnatin kasar take son dauka na kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila, inda suke kallo hakan a matsayin babbar cin amana ga al’ummar Falastinu.

Haka nan kuma bayanin nasu ya yi ishara da cewa, daukar irin wannan mataki ya yi hannun riga baki daya da manufar juyin da al’ummar kasar suka yi, wanda shi ne ya kawo masu na yanzu kan kujerar mulkin kasar, domin kuwa mutane ba sun kori Albashir ba ne domin su kulla kawance da Isra’ila.

Sabbin mahukuntan an sudan dai suna hankoron samun kusanci da gwamnatin yahudawan Isra’ila, duk kuwa da cewa sakamakon matsin lamba na al’ummar kasar, sun kasa fitowa fili su gaya wa jama’a abin da suke yi tare da Isra’ila a bayan fage.

3919506

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: fitowa ، ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: